RFI Hausa
@ha.rfi.fr
45 followers
6 following
3.2K posts
🌍 Sashen Hausa na RFI na maraba da ku a shafin Bluesky
💻 rfi.fr/ha/ 🎧 rfi.my/kai-tsaye
𝕏 rfi.my/Xha 📷 rfi.my/IGha 🗨️ rfi.my/WAha
Posts
Media
Videos
Starter Packs
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 2h
Ƴansanda sun kama Ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore a wata kotu da ke Abuja
Rahotanni na tabbatar da cewa ƴansanda sun kama Ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore a wata kotu da ke Abuja.Sowore ne dai ya jagoranci zanga-zangar neman a saki mai fafutukar kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu a ranar Litinin, kuma an ga lokacin da yake gudu yayin zanga-zangar da rahotanni suka tabbatar da cewa an kama wasu daga cikin waɗanda suka fantsama tituna a wannan rana.
rfi.my
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 6h
Bincike ya nuna cewa za a samu ƙarin ranaku 57 masu tsananin zafi a duk shekara
Wani sabon binciken ƙwararrun masu hasashen yanayi, ya ce za a samu ƙarin ranaku 57 masu tsananin zafi a duk shekara daga yanzu, waɗanda suka zarce makamantan su da aka samu daga shekarar 1991 zuwa 2000 sakamakon sauyin yanayi.
rfi.my
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 7h
Galatasaray ta yabawa Osimhen kan bajintar da ya yi a a karawarsu da Bodo/Glimt
Ƙungiyar Galatasaray ta yabawa ɗan wasan gabanta Victor Osimhen, inda ta ce babu wani ɗan wasan gaba daya kai shi a yanzu, bayan da ya samu nasarar jefa kwallaye biyu a karawar da suka yi da Bodo/Glimt a gasar zakarun Turai.
rfi.my
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 8h
Al'umma Nijar sun runguma tsarin amfani da hasken rana wajen samar da lantarki
A Jamhuriyar Nijar, yanzu haka ɗimbin mutane ne ke rungumar tsarin amfani da hasken rana wajen samar da lantarki da aka fi sani da Solar, wannan kuwa baya rasa nasaba da saukin wannan tsari da samuwarta a kowane lokaci.
rfi.my
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 20h
Faransa ta tanadi jami'an ƴansandan da za su bai wa Sarkozy kariya a gidan yari
Ministan harkon cikin gida na Faransa Laurent Nunez, ya ce za a aje jami’an ƴansanda biyu a kusa da ɗakin da ake tsare da tsohon shugaban ƙasar Nicolas Sarkozy, don bashi kariyar da ta kamata.
rfi.my
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 22h
Kotun tsarin mulkin Kamaru ta ɗage ranar bayyana sakamakon zaɓen ƙasar
Kotun tsarin mulki a Kamaru, ta ce sai ranar Litinin ne za ta bayyana wanda ya yi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasar tsakanin Paul Biya da Issa Tchiroma Bakary, da aka gudanar a ranar 12 ga watan Oktoban nan da muke ciki, saɓanin gobe Alhamis da a farko aka sanar.
rfi.my
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 23h
Cutar Lassa ta kashe mutane 172 a sassan Najeriya cikin 2025- NCDC
Hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta tabbatar da alƙaluman mutane 172 a matsayin waɗanda zazzaɓin Lassa da ɓera ke yaɗawa ya hallaka a sassan ƙasar cikin shekarar da muke ta 2025.
rfi.my
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 1d
Ƴan takara huɗu da ke ƙalubalantar shugaba Ouattara a babban zaɓen Ivory Coast
Lokaci na ci gaba da ƙaratowa a babban zaɓen Ivory Coast da ke tafe ranar 25 ga watan da muke na Oktoba, a wani yanayi da ƴan takara guda 4 ke shirin ƙalubalantar shugaba Alassan Ouattara a zaɓen, ciki har da mai ɗakin tsohon shugaba Laurent Gbagbo wato Simone Gbagbo.
rfi.my
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 1d
Ƴan takara 4 da za su ƙalubalanci Ouattara a babban zaɓen Ivory Coast
Lokaci na ci gaba da ƙaratowa a babban zaɓen Ivory Coast da ke tafe ranar 25 ga watan da muke na Oktoba, a wani yanayi da ƴan takara guda 4 ke shirin ƙalubalantar shugaba Alassan Ouattara a zaɓen, ciki har da mai ɗakin tsohon shugaba Laurent Gbagbo wato Simone Gbagbo.
rfi.my
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 1d
Ana kokonton ganawar Trump da Putin bayan Rasha ta faro atisayen soji mafi girma
Ukraine ta tabbatar da mutuwar mutane 6 a harin da Rasha ta kai mata da tsakaddare, harin da ke zuwa kwana guda bayan fitar wasu bayanai da ke cewa Amurka za ta jinkirta batun ganawar Putin da Trump, a wani yanayi da Moscow ta faro wani atisaye soji mafi girma da ya ƙunshi makaman nukiliya.
rfi.my
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 1d
Gasar Zakarun Turai: Barcelona ta ragargaza Olympiacos da 6 - 1
Fermin Lopez ya ci kwallaye uku rigis, yayin da Marcus Rashford ya ci biyu a wasan da Barcelona ta yi kaca-kaca da Olympiacos da ci 6 -1 ranar Talata, abin da ya sa ƙungiyar ta Catalan ta dawo kan ganiyarta a gasar zakarun Turai.
rfi.my
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 1d
An sanya ranar zaɓe a Uganda inda Shugaba Museveni zai nemi tsawaita mulkinsa
Hukumar zaɓen Uganda ta sanya ranar 15 ga watan Janairun shekara mai zuwa a matsayin lokacin da za a gudanar da zaɓen ƙasar, inda Shugaba Yoweri Museveni zai nemi tsawaita mulkinsa zuwa kusan rabin ƙarni.
rfi.my
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
· 1d
Harin mayaƙan RFS ya kawo tsaiko ga shirin buɗe filin jirgin saman Khartoum
Mayaƙan RSF sun kai hari da jirage marasa matuƙa kan filin jirgin saman Khartoum babban birnin Sudan, dai dai lokacin da ake gab da sake buɗe shi bayan kasancewa a kulle sama da shekara biyu da suka gabata.
rfi.my